EKITI 2018: Za a tura ‘yan sanda 30,000 domin zaben gwamna a ranar Asabar

0

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta girke jami’an ta har 30,000 a jihar Ekiti domin kula da yadda zaben ranar Asabar mai zuwa ke gudana.

A jihar Ekiti dai za su yi zaben gwamna ne a ranar Asabar, biyu bayan cikar wa’adin gwamna Ayodele Fayose.

‘Yan sandan da za a tura jihar sun hada da masu kwantar da tarzoma, Na Musamman, ‘Yan sandan Dalike Harin Ta’addanci, Masu Zakulo Bama-bamai da kuma Karabiti, duk za a tattara zuwa Ekiti.

Sauran sun hada da ‘yan sandan leken asiri da kuma karnukan sintiri.

Bayan su kuma za a aika da jiragen helikwafta biyu, motar daukar zaratan yaki guda uku, sai wasu kananan motocin daukar zaratan guda goma.

Za kuma a tura motocin ‘yan sanda har 250 da za su rika sintiri a akan titina.

Jawabin da Kakakin ‘Yan sanda na Kasa, Jimoh Mosheed ya fitar ya ce an kuma tura Mataimakin Sufeto Janar mai lura da Ayyuka na Musamman, domin ya je jihar a kula da yadda zabe ke gudana.

Akwai kuma wasu kwamishinoni 4, Masu Taimaka wa Kwamishina 8 sai Mataimakan Kwamishina 14.

Ya ce zai yi sa-idon ganin yadda ayyukan na su ke gudana a fadin rumfunan zaben jihar 2,451 da ke cikin mazabun jihar 177 cikin kananan hukumonin jihar guda 16.

Share.

game da Author