Dalilin da ya sa Ministar Kudi, Kemi ke yi mana duk abin da muke so -’Yan Majalisa

0

Wasu ‘Yan Majalisar Dattawa sun bayar da karin haske dangane da yadda Ministar Kula da Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ke biya musu bukatun su na bilyoyin kudade, sau da dama ba tare da son fadar shugaban kasa ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta sha bugawa da fallasa yadda ministar ke dumbuza wa ‘yan majalisar kudade ratata, har ma da biyan su kudaden kwangilolin da ko sa hannun amincewa da su ba a kai ga yi ko ba a ma yi ba dungurugum.

A cikin watan Afrilu na wannan watan ma an buga rahoton yadda ta sakar musu naira bilyan 10 a bagas.

Su kuma ba su bata wani lokaci ba, sai suka rika sayen zunduma-zunduma motocin balle-bushasha da kudaden.

An samu wasu sanatoci biyar da suka yi magana da wannan jarida, inda suka tabbatar da cewa manyan shugabannin majalisar ne ke barankyankyamar sa Kemi ta saki kudaden.’’

“Ai ba mu taba dacen samun Ministar Kudi wadda ke saurin biya mana bukata ba kamar wannan ta zamanin Buhari. Amma maganar gaskiya, an gano wani gyambo ne mai doyi da ta ke da shi, amma ta sa bandeji ta daure, ba ta so gwamnati ta ji warin.

“To dalili kenan duk lokacin da aka mika mata kofi, bangajin daro ko duro aka ce ta cika da kudi, sai ta kamfato kawai ta cika, ta miko.”

Wani babban sanata ya ce, “An rike wa Minista Kemi makogaro ne, da an dan shakare mata wuya, sai kawai ta saki kudi, don a saki wuyan ta.”

Amma dai ya ce bai san irin barnar da ta tafka a boye ba da har ake amfani da laifin ake tatsar kudi daga wurin ta ba.

“Ba komai muka sani ba, amma dai babu ruwan mu da sai mun san laifin da ta yi, tunda duk abinda aka roro ana rabawa da kowanen mu.”

An ce ministar ta na tsoron bincike daga Majalisar Dattawa, domin idan suka fallasa ta, za ta rasa aikin ta ne, tsige ta za a yi kawai.

PREMIUM TIMES ta gano cewa manyan shugabannin majalisar dattawa ne kawai suka san bahallatsar da Kemi ta boye ba ta so a sani. Su kuma sai suke amfani da wannan suka maida ta saniyar-tatsa.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya karyata zargin cewa su na maida ta saniyar-tatsa, kuma ba su san ta aikata komai ba.

Share.

game da Author