Dalilin da ya sa El-Rufai ya ke fushi da Saraki – Sanata Ibrahim

0

Sanata Rafiu Ibrahim ya bayyana cewa wasu daga cikin dalilan da yasa gwamnan jihar Kaduna ya ki jinin majalisar dattawa shine don ta ki amince masa da ya karbi bashi daga bankin duniya.

Idan ba a manta ba Sanatocin Kaduna duk ukun su sun ki amincewa wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya karbi bashin Dala miliyan 350 daga bankin duniya.

Wadannan kudade ya yi niyyar saka su wajen ginawa da raya jihar ne. Sai dai kuma kash, wannan buri tasa bai cika ba domin majalisa a wancan lokaci ta yi watsi da wannan batu.

Shi kuwa sanata Rafiu Ahmed da ke wakiltar Jihar Kwara a martini da ya maida wa El-Rufai game da cewa da yayi wai ba a taba samun tabarbararriyar majalisar dattawa ba kamar irin ta Bukola Saraki, ya ce,

Nasir El-Rufai

Nasir El-Rufai

“ Ai shi El-Rufai bakin sa bata da linzami, domin kuwa gatse yake magana. Ina so mutane su sani cewa shi El-Rufai na daga cikin wadanda suka rikirkita jam’iyyar APC har ta fada wannan matsala da take ciki.

“ Shi ba zai dai na surutu ba tunda ya gaza samun bashi daga bankin duniya, wanda kuma sanata dake wakiltar Kaduna ne yake shugabantar wannan kwamiti da taki amincewa da a bashi wannan bashi.

“ Ko da ya turo ministan kudi, ta tattauna da Saraki kan maganar samun amincewar majalisar game da bashin, da kan sa Saraki ya fadi mata ay shi ba shi da yadda zai yi a kai. Sai dai yace mata zai bata shawara da ta gaya wa gwamna El-Rufai ya koma ya tattauna da sanatocin sa su sami daidai tuwa akai, idan ko ba haka ba babu yadda zai iya nuna fin karfin iko akan sanatoci uku gaba daya a jihar ka idan suka ki amincewa da bukatun jihar da suke wakilta.

“ Ina sane cewa gwamna El-Rufai ya aika wa shugaban majalisa Bukola Saraki sakon nuna godiya da shawarwarin da ya bashi a lokacin da ya bukaci wannan bashi. Amma kuma saboda surutun tsiya gwamna El-Rufai yanzu ya fito yana fadin wani abin da ban.” Inji Sanata Rafiu

Sai dai kuma da aka ne ji daga bakin kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan, y ace har yanzu basu ga wannan takarda ta sanata Rafiu Ahmed ba da irin zantukan da ya furta game gwamna El-Rufai. Ya ce baya bukatar mu sanar dashi domin suna da hanyar da suke bi domin samin bayanan su.

Kaduna Senators

Kaduna Senators

Share.

game da Author