“Ina jin tsoro Jaki a Iraqi ya yi tuntube saboda Umar bai yi masa hanya ba.”
Babu shakka shugabanci al’amari ne mai girma, wajibi daga cikin mayan wajibai, kuma shine mafi hadarin duk wata jarabawan duniya, domin rayuwar Al-Ummah, jin dadinsu da walwalansu gaba daya sun rataya ne akan jagorancin shugaba.
Amirul Mu’minin Umar Dan Khattabi (R.A) ya kasance madubin dubawan mahukunta Musulmai da wadanda ba Musulmai ba, saboda gaskiyarsa, rikon amanarsa, jajircewarsa, tsantseninsa da tsare-tsare na mulki da ya kawo wadanda a halin yanzu a kafi amfana da su a Yammacin duniya, wanda bayaninsu na nan tafe daki-daki.
Lokacin da aka shugabantar da Umar Dan Khattabi (RA) sai ya sanar cewa shi ba zai karba albashi ba, duniyar za ta wadatar da shi, amma bayan kama harkar shugabanci sai ya shagala da hidimar Al-Ummah ya bar cigaba da kasuwancinsa har dukiyarsa ta kare. Sai ya zauna da manyan Sahabbai irinsu Usman Bini Affan, Aliyu Ibini Abi Talib, AbdurRahman Ibini Awf, Sa’ad Ibini Abi Waqas dss, yace:
“Da nace muku ba zan dauki komai daga Baitul Mali a matsayin albashi ba saboda dukiyata ta wadatar da ni amma yanzu ta kare, mene abunda zan iya samu daga Baitul Mali a matsayin albashi da alawus?
Suka amsa masa da cewa: “Amirul Mu’minin yafi mu sanin yadda ya kamata.”
Sai yace: “Abun hawa (rakumi ko wanninsa) da nake butaka zuwa Hajji ko Umara, tufafi kala biyu na lokacin zafi da tufafi biyu lokacin sanyi da abincin iyalina sannan hakkina na alawus-alawus ake ba dukkan Musulmi, domin nima ina daya daga cikinsu.”
Sahabbai suka ce: “Wannan shine adalci”, yace, “dukkansu kun yarda da wannan” suka ce, “Eh”.
Wani mutum daga gefe ya tsoma baki yace: “Ya Amirul Mu’minin, “Wanda yafi cancanta ya samu abinci mai kyau, abun hawa nagartacce da kaya masu kyau, kai ne”.
Khalifa Umar Dan Khattibi (RA) ya ba shi amsa da cewa: “Wallahi ina kyautata zaton ba don Allah ka fadi haka ba sai don samun kusanci a wurina, na kasance ina kyautata maka zato, ka san matsayina da wadannan (mutane dake wurin) kuwa? Misalin wasu mutane ne da suka yi tafiya tare, sai suka danga kudadensu a hannun daya daga cikinsu, suka shugabantar da shi akan dawainiyarsu (na abinci da sauran bukatu). Shin ya halatta ya dauki wani abu fiye da na sauran?” Sai mutumin yace, “A’a”, sai Umar (RA) yace, haka tsakanina da wadannan yake”. Allahu Akbar!
Abunda wannan gajeruwan qissa ke nuna mana shine, kada shugaba ya rudu, ya mayar da dukiyar Al-Ummah kamar mallakinsa, yana sarafata yadda yaga dama bisa son rai, domin idan ya yi haka, to dako ne yake tara ma kansa Ranar Al-Kiyama. Ga dakon kaya ga mari-mari (cikin sarqa).
Khalifa Umar (RA) ya dauka ma kansa nauyin zama Uba ga dukkan iyalan Musulmi. Saboda haka yake sintiri da kansa lungu da sakon Madina dare da rana, bisa yaqininsa Allah Yana kallon aikinsa dare da rana.
Wata rana yana yawo sai ya riski wata wata a waje-wajen gari cikin tanti da yaranta kanana tana sabibin cewa Allah ne zai shiga tsakanin su da Umar. Sai ya yi maza yace mata, “Subhan-Allah! Me Umar ya yi muku?” sai tace, “Allah ya shugabantar da shi akan mu ya bar mu da yunwa”. Sai yace mata, “to mene ne a cikin tukunyar da kika daura a kan murhu”? Sai tace, “ruwa ne da duwatsu a ciki, ina yin haka ne saboda su saka rai za su ci abinci har barci ya kwashe su”.
Nana take ya bazama sai Baitul Mali ya dauko buhun abinci a kafadansa ya zo da shi ya dafa musu da kansa ya ciyar da yaran da kansa. AbdulRahman Ibini Awf (RA) wanda ya yi masa rakiya yace: sai da na yi kuka ganin yadda Umar ya tsuguna ya dage wurin hura murhu hayaki ya cika masa ido da gemu.
Bayan haka yace gobe ta nemi inda Amirul Mu’minin yake za’a saka su a cikin jadawalin marasa karfi, alhalin bata san shine Umar din ba.
Haka nan ma ya taba riskan wata mata mai shayarwa da ta yi kokarin yaye danta karfi kafin lokacinsa saboda a saka shi a cikin yaran ake basu alawus-alawus. Yace mata, “Yar uwa, ba zaki rarrasheshi ba? Sai tace, ai yayensa nake son yi”, yace mata, “saboda me? Ya yi karami a yaye shi”, sai tace, “Umar ba ya bada alawus-alawus ga yaran da ake shayarwa sai wadanda aka yaye su” Yace, “Subhan-Allah! Umar ‘ya’yan Musulmi nawa ka kashe da wannan tsari naka?”
Nan-da-nan ya yi sanarwa cewa daga yanzu har yaron da ake shayarwa za’a saka shi a jadawalin alawus alawus. Allahu Akbar!
Wannan kadan daga cikin salo da tsarin mulki irin na Umar Dan Kattabi (RA) kenan. Fitowa na gaba za mu ga tsare-tsare da ya kawo wadanda har yanzu ake amfana da su, musamman a “Yammacin Duniya” da matakan da ya bi ya hana cin hanci da rashawa a zamanin mulkinsa.
Allah muke roko Ya cigaba da datar da mu da abunda yake so kuma Ya yarda, Ya karbi wannan aiki a matsayin Sadaqah Jariyah, ameen.
Magajin Mallam: Abu Yahya (Aslam)