Da an gina ‘Alkaryar Fim’ da wasu matsalolin sai dai mu ji su, ba a Kannywood ba – Ummah Shehu

0

Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Ummah Shehu ta koka kan rashin gina katafaren Alkaryar Fina-finai a matsayin daya daga cikin babbar matsalar da ya sa a ake samun tabarbarewar harkar fina-finai a yanzu da ake fama dashi a farfajiyar.

A hira da tayi da PREMIUM TIMES, ummah ta ce da Allah ya sa sun sami wannan Alkarya da yanzu kakar su ta yanke saka a harkar shirya fina-finai na Kannywood.

PT:Me nene kike ganin ya sa ake samun karancin kasuwar fina-finan Hausa a yanzu?

Ummah: A matsayina na ‘yar wasa kuma mai shirya wa, ina tabbatar maka cewa karancin fitowar fina-finai ne babban matsalar mu sannan kuma hakan ya samo asali ne saboda fama da muke yi da barayin basira wato Piracy. Da zarar ka fidda fim sai suyi mata ca kamar kudan zuma su buga shi suna siyar wa tun kafin kai ka mori gumin ka sun cinye har sun side tas.

Na biyu kuma sai rasa Alkaryar Fim da muka yi. Wannan abu da ya fidda mu wadannan matsaloli da muke fama dasu a yanzu.

PT: Menene ya sa ba a gina shi wannan Alkarya ba?

Ummah: Damar da muka samu ce ta sullube mana muna ji muna gani babu yadda za muyi. Tun a shekarar 2016 ne aka yi niyyar fara aikin gina wannan Alkarya da zai ci naira Biliyan hudu amma abin bai yiwu ba saboda siyasa da ta dabaibaye wannan aiki da zai amfane mu.

Shi wannan Alkarya da an gina shi zai samar wa masu shirya fim guraren hada fim, karanta don ‘yan wasa, shirya fina-finai, sinima, hada hotuna, wajen koyan aiki da kwarewa da dai sauran su. Abin zai zamo kamar Hollywood ne irin ta kasar Amurka. Amma sai gashi yau an wayi gari mun tashi a tutar babu.

PT: Yanzu babu dabarar da za ku iya yi don gabatar da wannan magana ga wasu da kuke ganin kila a dawo da maganar gina alkariyar kuma?

Ummah: Ina ganin ai yanzu bakin alkalami ya bushe domin ko a wancan lokacin anyi ta kai ruwa rana saboda wannan abu. Malamai sun fito sun kushe abin.

PT: Yanzu menene mafita?

Ummah: Mafita ita ce mu ci gaba da yaki da barayin ayyukan mu da suke zuwa su buga su siyar, daga nan sai kuma mu nemi taimakon gwamnati. Domin sune kawai zasu iya taimaka mana wajen ganin an fatattaki wadannan mutane da ‘yan kasuwa.

PT: Da wadannan kalubalai da farfajiyyar ke fama da su yaushe ki ke ganin za ki iya sakin fim din da ki, ‘Burin SO’?

Ummah: Batare da bata lokaci ba zan gabatar da sabuwar fi dina da zarar na kammala aiki a kai.

PT: Yanzu kina nufin ba ki tsoron masu masu satan fasaha, wato Piracy ganin kin kashe miliyoyin kudaden da kika kashe?

Ummah: Ni ba haka nike ba, Ina tabbatar maka fim ne mai inganci kuma mashahuri, zai kuma nishadantar da masu kallo. Saboda haka zan bi duk hanyoyin da ake bi sauran kuma in bar ma sarki Allah.

PT: Kin san cewa ynazu mafi yawan masu kallon Fim din Hausa sun koma kallon Fina-finan indiya da Chana da aka fassara su da harshen Hausa, saboda ba su samun naku a kasuwa, Me zaki ce kan haka?

Ummah: A gaskiya hakan na ci mana tuwo a kwarya amma yaya za muyi, mutum ba zai saka kudin sa a harka fim ba sannan wani ya kwankwade masa romon har da kashe kwano. kaga ai ba haka aka so ba. shine ya sa dole sai anbi abin a hankali tukunnan sannan komai zai gyaru. Amma yanzu kam abin da kamar wuya. Ka ga da ace mun dace da samun Alkaryar Fina-fina da duk ya warware mana irin wadannan matsaloli.

PT: Kina nufin idan ba an samar muku da alkariyar ba babu abin da ku ‘yan fim za ku iya yi kan haka?

Ummah: Ina dole ne nemo mafita kuma an ta kokarin yin haka. Manya daga cikin Kannywood suna kokarin tallata ‘yan wasan Kannywood a wurare da yawa musamman a harkokin da ya shafi nishadi kamar fina-finai da sauran su. Idan Ka kula irin wadannan gudunmuwa ne jarumai kamar su Ali Nuhu, Rahama Sadau, Sani Danja, Yakubu Muhammed, Usman Uzee da sauran su suke badawa domin jawo hankalin masu saka jari su karkato su waiwaye mu. Kaga ai haka shima ci gaba ne domin nuna mu yake yi cewa akwai basira kwararru a farfajiyar fina-finan Hausa.

Bayan Haka dole mu jinjina wa jaridar PREMIUM TIMES, domin kuwa tana bamu gudunmuwa matuka wajen tallata mu a idanuwan duniya. A haka zaka wasu masu saka jari sun waiwaye kannywood din sun hada hannu da mu da gwamnati sai kaga an ci gaba.

Share.

game da Author