Bincike ya nuna cewa cin man kifi wanda ake kira ‘Omeg 3 Supplements’ a turance baya cutar da masu fama da cutar zuciya.
Wasu masu yin nazari da bincike a fannin kiwon lafiya dake kasar Britaniya suka gano haka bayan sun gudanar da bincike kan ko akwai illolin da cin man kifi ke yi a jikin mutane 112,059 musamman wadanda dake fama da matsala a zuciya.
Bayan haka kuma bayanan binciken sun nuna cewa tabbas ba ta yi wa jiki lahani musamman masu dauke da cutar a zukatan su mai makon haka ma lafiya yake kar wa mara lafiya sannan ya samar masa da kariya.