A yau Talata ne Kungiyar Hadin kan Kasasshen Afrika ta Yamma ECOWAS ta za bi shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari sabon shugaban kungiyar.
An zabi Buhari ne a taron kungiyar da ya gudana a kasar Togo.
Buhari ya yabi shugaban kungiyar mai barin gado wato shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe sannan ya ce zai ci gaba da kyawawan ayyukan da kungiyar ta sa a gaba domin ci gaban kasashen yankin.