Shugaba Muhammadu Buhari ya nesanta kan sa daga daga wani yunkuri da ‘yan majalisar jihar Benuwai marasa rinjaye suka yi da nufin tsige gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.
A cikin wani jawabi da kakakin sa Femi Adesina ya fitar, ya ce, “Shugaba Muhammadu Buhari ba zai taba tsoma kan sa ko shiga cikin wani sha’ani da ba ya cikin dokar kasar nan. Kuma duk wani kokarin a danganta shi da abin da ya faru a jihar Benuwai, to ba zai yi nasara ba.”
Buhari da jam’iyyar sa APC su na ci gaba da shan suka ganin yadda aka yi amfani da jami’an tsaro na ‘yan sanda, aka hana ‘yan majalisa 22 shiga cikin zauren majalisa, alhali aka bai wa 8 kariya shiga su yi zaman tura wa Gwamna Ortom takardar sanarwar tsigewa.
Mambobin takwas na APC dai sun zargi Ortom da laifin wawuran kudade, inda shi kuma ya karyata zargin na su.
Dimbin jama’a ne suka yi Allah-wadai da yadda aka yi amfani da ‘yan sanda a kokarin na tsige gwamnan jihar Benuwai, Ortom.
Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara duk sun yi tir da yunkurin wanda suka ce ba ya kan tsarin da dokar Njariya ta shimfida.
Adesina ya ce bai kamata a jefa sunan Shugaba Buhari a cikin wannan kwatagwangwamar siyasar jihar Benuwai ba.
Ya ce abin da ke faruwa a yau a kasar nan, idan wasu su ka kunno wuta, idan ta yi musu dadi, sai su yi ta murna, idan kuma ba ta yi musu dadi ba, sai su dora laifin a kan shugaban kasa. Idan ta yi musu zafi kuwa, sai su fara kururuwar shugaban kasa ya zo ya kashe musu wutar.”
“Shi Shugaba Buhari ba zai taba tsoma kan sa cikin duk wata kwakyariyar da ba ta da nasaba da tsarin da dokar kasa ta shimfida ba.”
Discussion about this post