Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar jirgin kasa a Abuja, babban birnin tarayya.
Buhari ya kaddamar da tashar a yau Alhamis da safiya, a sabuwar tashar wadda aka gina a Central Area, Abuja.
Jim kadan bayan bude tashar,shugaban kasa tare da wadanda suka rufe masa baya da tawagar ‘yan jarida sun shiga jirgin daga tashar da ke Central Area zuwa Babban Filin Jirgin Sama na Abuja.

Wannan titin jirgi dai shi ne na farko a Abuja, babban birnin tarayya.
Ya zuwa yanzu kenan an kaddamar da titi daya, wanda zai rika zirga-zirga da kuma jigilar fasinja da filin jirgi zuwa Abuja, da kuma Abuja zuwa filin jirgin na sama.
Daga Abuja dai kuwa filin jirgin saman birnin, kusan tafiya ce ta kilomita wajen 40.

