Jam’iyyar APC ta Hakika ta bayyana cewa kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari da Adams Oshimhole ke yi don sasantawa kada hasalallun cikin su su fice daga jam’iyyar, ai sun makara domin alkalami ya rigaya ya bushe.
Cikin wata takarda da kakakin R-APC, Kassim Afegbua ya sa wa hannun, ya ce shugaban su Buba Galadima ya ce ba za su taba sasantawa da APC ba.
“Ai Buhari da Oshimhole sun makaro, sun yi sake har jirgin ya cira sama.
“Masu iya magana sun cewa damisa ba ta taba canja launin jikin ta.”
Haka Afegbua ya kwatanta halayyar mulkin Buhari da na jam’iyyar APC.
“Kowa ya gane su saboda sun saba yin alkawari su na karyawa. Don haka ba za mu yarda su yaudare mu ba.
“Sun ma yaudari talakawa suka yi musu alkawurra, tun a cikin 2015 amma har yanzu shiru, to ina ga mu!
“Da Buhari ya samu mulki ai mike kafa ya yi a cikin Villa, ya bari ana wulakanta mu, aka manta da mu. Sai yanzu da ya ga zabe ya zo sannan zai fito ya sake yi mana romon-kunne? To ba za mu yarda ba.”