Buba Galadima dan rudu ne kawai yana neman inda zai makale ne – Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa idan dai don rudun da Buba Galadima ya ke yi ne game da jam’iyyar APC wai bata yi masa adalci ba toh ya je can ya karata domin korafin sa ba zai yi tasiri a Jam’iyyar ba.

” Shi fa Buba Galadima kamar tsuntsu ne da ya dimauce a cikin tsakiyar daji shi bai yi gaba ba bai yi baya ba sannan kuma ga ‘yan farauta nan sun zagaye shi suna ta busa kaho ana kina an hango nama.

” Wadanda suka cancanci mu tattauna da su muna nan muna neman a sulhunta amma ba yan kwashi-kwaraf ba masu neman suna.

” Kada wani ya karaya saboda wani wai Buba Galadima, babu abin da zai iya yi da makarraban kan mu a 2019.

” Mutanen Najeriya sun amsa kira kuma suna tare da manufofin gwamnatin Buhari musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa. Anan kowa ya san an sami nasarorin gaske kuma a haka za a ci gaba da tafiya.

Share.

game da Author