Boko Haram sun kawo tsaikon shata kan iyakar Najeriya da Kamaru – UN

0

Batun kara tantance kan iyakar Najeriya da Kamaru da majalisar Dinkin Duniya ke yi ya na samun tsaiko saboda matsalar tsaro daga barazanar Boko Haram a yankin da matsalar ta shafa.

Wannan bayani ya na kunshe ne cikin wani rahoto da Babban Sakatare mai kula da Afrika ta yamma da kuma yankin Sahel.

Antonio Gutteres ya kara da cewa tashe-tashen hankulan da ke kara faruwa a yankunan kasashen da ke magana da Turanci a yankin Kamaru, shi ma abin dubawa ne, kuma babban kalubale ne.

“Wadannan matsalolin kawo mana tsaiko wajen kara shara kan iyakar tare kafa kakkafa dirkoki a kan iyakar. Amma duk da haka, mun yi wata ganawa a Lagos ranar 19 da 20 Ga watan Maris, inda muka karkare yadda za mu karfafa matakan tsaro domin ci gaba da aikin da ke aiki.”

Share.

game da Author