BIRNIN GWARI: ‘Yan sanda biyu, mahara biyu su rasu a batakashi

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa rundunar ta rasa jami’an ta biyu a batakashi da suka yi da wasu ‘yan bindiga a dajin Birnin-Gwari zuwa Funtua.

Aliyu ya ce maharan sun ya wa jami’an ‘yan sandan kwantar bauna ne suka far musu a daidai suna sintiri a yankin.

Bayan batakashi da aka yi da su wadannan maharan, wasu jami’ai biyu sun rasu sannan an kashe mahara biyu.

Sai dai kuma bayan an kwashi gawan ‘yan sandan zuwa Kaduna ne aka sake samun wani hadarin inda bindigar wani jami’i ta tashi ba da sanin sa ba ta sami wata mata a jiki. Maza-maza aka garzaya da ita asibiti sai dai Allah yayi mata cikawa kafin a iya shayo kanta.

” Muna matukar juyayin rasuwar wannan mata da hadarin bindiga ya sameta, duk da cewa mun kai ta asibiti Allah bai yi za ta rayu ba.” Inji Aliyu.

Idan ba a manta ba rundunar ‘yan sandan Najeriya ta saka naira miliyan 5 ga duk wanda ya tona asirin wadanda suka kashe jami’an ‘ya sanda 5 a garin Abuja da Edo.

Share.

game da Author