Shugaban Muhammadu Buhari ya furta cewa babu abin da ya dame shi da masu ficewa daga jam’iyyar sa mai rike da mulki zuwa jam’iyyar adawa, PDP da wasu jam’iyyu.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga ‘yan Najeriya mazauna kasar Togo.
An yi wannan ganawa ce ido-da-ido a jiya Lahadi da dare, a Lome babban birnin kasar.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a yau Litinin a Abuja, a cikin wata takarda da ya fitar a Abuja.
Ya ce Buhari ya ce bai damu ba, saboda ‘yan Najeriya su na da kyakkyawan yakini a kan gwamnatin sa, kuma su na yaba muhimman ayyukan da ya ke yi da kuma kokarin da ya ke nunawa.
“Ina tabbatar muku da cewa mafi yawan ‘yan Najeriya can a gida su na yabawa da aikin da mu ke yi.”
Da ya ke nuna farin cikin sa ganin yadda dandazon ‘yan Najeriya mazauna Togo suka taru daga yankuna biyar na kasar, domin su gana da shi, Buhari ya yi murna da har ya ji yadda suke ba shi labarin irin gagarimin ci gaba da ya samar a Najeriya. Wannan ya nuna lallai, su na kasar Togo da zama, amma zuciyoyin su na Najeriya kenan.
Buhari ya shaida musu cewa da a ce gwamnatocin baya sun yi amfani da ko da kashi 25 bisa 100 na kudaden danyen man fetur, to da Najeriya ba za ta yi kukan komai ba a halin yanzu.
Har ma ya buga misali da dala biliyan 16 da aka salwantar wajen kokarin farfado da hasken lantarki, amma ba a samu hasken ba, sai karin duhu.
Ya yi musu alkawarin cewa za a sayar da dukkan dukiyoyi da kadarorin da aka kwato daga hannun wadanda suka wawuri dukiya, sannan a saka kudin cikin baitilmalin Najeriya.
Discussion about this post