Mashawarcin Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, a kan Ayyuka na Musamman, ya fice daga jam’iyyar APC.
Usman Bawa, da aka fi sani a Kaduna Shehu ABG, wanda ya taba yin dan majalisar Tarayya inda ya wakilci Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, ya fice daga APC ne a yau Litinin.
Ya aika da wasikar sanar da cewa ya fice daga jam’iyyar ne a ranar 14 Ga Yuli, inda sakon ya isa ga Shugaban APC na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.
Bawa ya fara aiki tare da Dogara a cikin 2015, tun bayan da aka nada shi kakakin majalisa.
Kakakin yada labaran Dogara, Turaki Hassan ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa.
Duk da dai bai fadi dalilin barin sa jam’iyyar ba, ya bayyana cewa zai yi gaba ne domin ya gusa daga inda ya ke.
Har yanzu dai bai ce ga jam’iyyar da ya tuma tsalle ya dirga a ciki ba.
Dama kuma cikin watan Yuni ne Hakeem Baba-Ahmed daga Kaduna shima ya fice daga APC.