APC ta nemi Saraki ya fito ya bayyana bangaren da ya ke

0

An kalubalanci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, da ya fito ya bayyana bangaren da ya ke a cikin jam’iyyar APC.

Mataimakin Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na kasa, Yekini Nabena ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya fitar ga manema labarai a Lagos.

Ya zargi Saraki da raba kafa tsakanin APC da kuma R-APC, wadda dama jam’iyyar APC ta zargi Saraki cewa shi ne ya kafa ta, kuma shi ne ya daura mata fika-fikan da ta ke faffaka da su.

Ya ce shugaban na majalisar dattawa na da ‘yancin ya yi alaka ko ya jingina da ko ma wane kowace jam’iyya, amma fa ya sani cewa akwai ka’idoji, kuma tilas ya bi su, ba haka kawai ya rika gudanar da aikace-aikacen da za su karya jam’iyya ba.

Daga nan kuma sai ya zargi Saraki da cin amanar jam’iyyar APC tare da yi mata tawaye da kuma zagon-kasa.

Ya kara da cewa har yau Saraki bai dauki darasi ba, tun bayan cin amanar da yay i wa APC a 2015, inda ya hada kai da PDP don ya samu kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, wanda haka ne kuma ya hana APC din samu kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Nabena ya buga misali da yadda makarraban Saraki biyu, Abubakar Baraje, da Hakeem Baba-Ahmed, wadan da suka fice daga APC, suka koma PDP.

Share.

game da Author