An kori masu tsintar bola daga Abuja

0

Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT), ta haramta wa masu tsintar bola bi kan titinan birnin su na tsintar shara a kwandunan sharar kofar gidaje.

Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran Ministan Abuja ya sa wa hannu, Abubakar Sani ya ce hakan ya biyo bayan korafe-korafen rahotannin sace-sace da ake zargin masu kwasar bolar na yi ne.

Sanarwar ta ce ana yawan zargin su da dibga kananan sace-sace, fashi da makami da sauran kananan laifukan da ba za a ci gaba da kauda kai a kan su ba.

Sakatariyar Hukumar Tsaftace FCT, Ladi Hassan, ta kara da cewa matasan da da aka fi sa Baban Bola, su na kuma yawan satar kayan gwamnati a wurare da dama, sannan kuma akwai su da kauda ajiyar da ba su ne suka yi ba.

Daga nan ta shaida cewa an amince su yi harkokin Baban Bola a garuruwan Gousa, Karshi, Bwari, Gwagwalada, Kwali, Abaji da Kuje.

A karshe ta yi kira ga jami’an tsaro su kama kuma su gurfanar da duk wanda suka kama ya na tsintar bola a cikin birnin Abuja.

Share.

game da Author