Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito daga Birnin Kebbi cewa an kori wasu malamai biyar na makarantar sakandaren Polytechnic Academic da ke a Birnin Kebbi, saboda yi wa wata daliba daya ‘yar shekarun karatun karshe ciki.
NAN ya ruwaito cewa ita ma yarinyar wadda ba a bayyana shekarun ta ba, ta na cikin wadanda aka kora daga makarantar.
Majiya ta tabbatar da cewa an dauki hukuncin korar su ne bayan kwamitin da aka kafa ya binciki lamarin ya gabatar da sakamakon binciken sa.
Kwamitin ne da kan sa ya ce a kori malaman su biyar da kuma dalibar.
Lokacin da kwamitin ya tuntubi wadanda ake zargin, dukkan su sun tabbatar da cewa lallai sun sha yin lalata da yarinyar, a lokuta daban-daban.
Sai dai kuma NAN ta ruwaito cewa malaman sun daukaka karar korar su a gaban hukumar gudanarwar makarantar.
Shugaban Makarantar, Mohammed Mahuta ya na jiyya a asibiti tun kafin faruwar al’amarin.
Amma mataimakin sa Oumar Woulandakoye ya tabbatar da korar malaman.
Discussion about this post