Hasalallun ‘yan jam’iyyar APC da wasu da suka kafa sabuwar PDP kuma suka narke cikin APC sun kafa sabuwar kungiya mai suna gyararriyar APC.
A jawabin da suka fitar yau bayan kammala taron musamman, Shugaban kungiyar sabuwar PDP a wancan lokaci Abubakar Kawu Baraje da jigo a tsohuwar jam’iyyar APC Buba Galadima sun bayyana cewa yin haka ya zama dole ganin yadda jam’iyyar APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa mutanen Najeriya.
“Idan ba a manta ba, a 2015, gamayyar jam’iyyu da kungiyoyin siyasa ne suka hadu domin a kafa wannan gwamnati na APC. Tun bayan haka abubuwan da jam’iyyar tayi wa mutane alkawari a kai suka kasa samuwa. In banda mulkin kama karya da ake yi da muzguna wa mutane da bakin talauci da ya addabi mutane, nan ne muka ga ya kamata mu kafa irin wannan kungiya domin a gyara idan har zai yiwu.
Bayanai sun nuna cewa hakan na da nasaba da shirin da wadannan gungun jigajigan ‘yan siyasa komawa jam’iyyar PDP domin tunkarar Buhari da makarraban sa a 2019.
Idan ba a manta ba tun bayan rantsar da wannan gwamnati ne ake ta takun saka tsakanin shugaban kasa da wadannan jiga-jigan yan jam’iyyar wanda da yawa daga cikin su sun koka ne kan watsi da su da aka yi da kuma nuna halin ko in kula da jam’iyyar tayi musamman shugaban kasa.
A makon da ya gabata tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa shi kadai tal, da jam’iyyar PDP za su iya kada Buhari, wanda a martanin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fitar daga baya kuwa ya bayyana cewa ko karamar hukumar sa ma ba zai iya kawo ba a 2019.
Yanzu dai kungiyar da nan tana ganawa a tsakanin mambobin ta da sauran ‘yan jam’iyyar APC da ke cike fam da fushi kan yadda aka mai dasu saniyar ware.
Discussion about this post