An daure wani matashi a dalilin barazanar kisa da yake yi wa makwabcin sa

0

Kotu dake garin Karmo a Abuja ta yanke wa wani matashi mai suna Felix Okon dan shekara 22 hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni biyar.

Kotun ta yi haka ne bisa ga zargin barazanar kisa da shi Okon yake yi wa wani makwabcin sa mai suna Raymond mai shekaru 65.

Bisa ga bayanan da lauyar da ta shigar da karan Ijeoma Ukagha ta bayar ta ce Okon kan yi wa Raymond barazanar kisan a duk lokacin da ya sha giya ya bugu.

” Tun a watan Faburairu Okon yake yi wa wannan tsoho da iyalan sa barazana. Sannan kuma ya na ta cewa sai ya kashe su da bindiga.”

Bayan haka kotu ta ba Okon zabi ko ya zauna a kurkuku ko ya biya taran Naira 8000.

Okon ya amsa duk laifin da kotun ta zarge shi da sai dai ya roki sassauci da yin alkawarin nisanta daga shan giya da yi wa makwabcin sa barazanar kisa.

Kotu ta yanke wa Okon hukuncin zama a kurkuku domin sauran matasan dake yi wa na gaba da su rashin kunya su dauki darasi.

Share.

game da Author