Rundunar ‘Yan sandan Jihar Lagos ta damke wasu iyayen kananan ‘yan mata kwailaye biyu da kowanen su ya yi wa ‘yar sa fyade.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edgal Imohimi ne ya shaida wa manema labarai cewa daya daga cikin wadanda ake zargin ya sha yin lalata da ‘yar ta sa mai shekara 14 da haihuwa, kafin daga bisani ya aura wa wani direban sa ita, daga nan ta dauki ciki mai karancin shekaru, wato 14 kacal.
Ya ce jami’an tsaro sun kama uban yarinyar a inda aka ritsa shi cikin gidan wani mai maganin gargajiya, inda ya kai ‘yar ta sa mai shekaru 14 kuma ta na cikin halin nakuda.
Kwamishina har ila yau ya kuma bayyana kama wani uban wata karamar yarinya dan shekaru 40 da haihuwa, wanda direban bas ne shi ma, wanda ake zargin ya yi wa ‘yar sa mai shekaru 12 da haihuwa fyade.
An ce ya yi mata fyaden ne a unguwar Ketu, Lagos.
Ya ce wani mutumin kirki ne ya kai karar uban yarinyar ga ‘yan sanda bayan da ta gaji da yadda uban ke ta yawan lalata da ita, har ta gudu zuwa gidan mutumin.
Ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu, domin shari’a ta yi musu hukuncin girbar hatsin da suka shuka.
Discussion about this post