AMBALIYAR KATSINA: Sojojin Sama sun kai wa mutane 2, 000 agajin kula da lafiya a Jibiya

0

Hukumar Sojojin Saman Najeriya ta bayyana cewa ta fada aikin duba lafiya da kai kayan agaji ga mutane sama da 2,000 da ke zaman gudun hijira, sakamakon ambaliyar da ta afku a garin Jibiya, cikin jihar Katsina.

Daraktan Hulda da Jama’a na sojojin sama, Olatokumbo Adesanya ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Adesanya ya kara da cewa aikin duba lafiyar masu zaman gudun hijirar ya na gudana ne a babbar firamare ta garin Jibiya.

Ya ce wannan wani kokari ne da Babban Hafsan Sojojin Sama na Kasa, Sadiq Abubakar ya shigo da shi.

A cewar sa, wannan shiri ne domin agaza wa masu gudun hijira domin rage musu wasu bangarori na wahalhalu da damuwa, musamman bangaren kulawa da lafiyar su, sakankancewa wadannan dubban masu zaman sansanin hijira sun rasa wuraren zaman su.

Kakakin na sojojin sama, ya kara da cewa sun gamsu da irin yadda jama’a suka karbi shirin hannu biyu, kuma sun nuna godiya matuka.

“An duba lafiyar kananan yara da dama, kuma an raba gidajen sauro da magunguna.

Kuma an raba tabarau ga wadanda aka yi wa aikin ido.

Share.

game da Author