Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya bayyana cewa ambaliyar da ta afku a Karamar Hukumar Jibiya, ta ci rayuka 44, yayin da har yanzu ana neman wasu mutane 20 ba a kai ga gano su ba.
Masari ya bayyana haka ne a yammacin Litini bayan ya kai ziyarar jaje a yankin da ambaliyar ta afku.
Ya kara da cewa an yi asarar dabbobi masu yawa yayin ambaliyar, wadda ta afku sakamakon ruwan da aka rika shekawa da daren Lahadi, har sama da awa uku.
“Ni dai da ido na ban taba ganin irin wannan mummunan bala’i ba.” Inji Masari a cikin jimami.
“Tsawon tashin ruwan sama da ya yi toroko, ya kai kafa goma. Sai dai mu ce wannan ibtila’I ce daga Allah kawai, domin duk mun gina magudanan ruwa da kai kwararar da ruwa a cikin Kogin Jibiya.
“Amma ruwan da ke malalawa cikin kogin ne ya rika dawowa da baya zuwa cikin gari.
“Na ga matashi ango sabon aure, kwana uku da daura aure, ya na ta fagamniyar neman amaryar sa. Abin ban-tausayi.
Tuni dai Masari ya ce an maida wadanda suka rasa matsugunan su zuwa firamare ta garin, kuma NEMA ta kai agajin gaggawa na kayan abinci da sauransu, har cikin mota 13.
Ya kuma yi kira ga Ma’aikatar Muhalli da a karkatar da ruwan, ta yadda zai daina kwarara a cikin kogin.
Kafin zuwan gwamna Masari garin Jibiya, shugaban hukumar NEMA na jihar Aminu Waziri ya sanar da afkuwar wannan ibtila’I da irin gudunmuwar da hukumar ta kai wa mutanen na gaggawa.
Ya bayyana cewa wannan ambaliya a fadawa kauyukan Tundun Takari, Dan Tudu, Unguwar Kwakwa da Unguwar Mai Kwari duk dake karamar hukumar Jibiya din.