Akalla mutane 400 ne aka yi wa gwajin cututtuka da ba su magani kyauta a jihar Legas

0

Ma’aikatan kiwon lafiya dake asibitin ‘Shell medical diagnostic center’ da likitocin dake jami’ar jihar Legas sun tallafa wa mazaunan unguwannin Lekki da Ogudu Ori Oke a jihar Legas da magunguna da gwajin cututtuka kyauta.

Jagoran wadannan ma’aikatan kiwon lafiya Chris Kwakpovwe a tsokacin da ya yi ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi haka ne domin taimaka wa talakawan jihar samun ingantacciyar kiwon lafiya.

Ya ce sun yi wa mutane gwajin cututtukan Kanjamau, Zazzabin Cizon sauro,hawan jini, Daji. Sannan da bada magunguna, gidaje sauro kyauta wa mutanen.

Ya kuma hori mutane kan yawai ta cin abin cin dake kara karfin garkuwan jiki sannan da yin gwaji akai- akai domin shawo kan cutar da ka iya kama su.

” Shan giya, zukar taba sigari da cin abincin da bai kamata ba na yi wa kiwon lafiyar mu illa domin banda cututtukan da suke kawowa sukan sa mutum ya tsufa da wuri.”

Share.

game da Author