Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da cutar Hepatitis B da C

0

Binciken ya kuma nuna cewa cutar bata nuna alamu idan an kamu da ita sai bayan ta kusa kashe mutum ko kuma ta hanyar yin gwaji.

Amma alamun cutar Hepatitis sun hada da canza kalar fatar jikin mutum zuwa kalar ruwan kwai, farin kwayar ido,amai, yawan jin gajiya a jiki,ciwon ciki,yawan zuwa bahaya da sauran su.

Abubuwa 9 da ya kamata a sani game da Hepatitis B da C

1. Cutar hepatitis B da C cututtuka ne dake kisan mutane miliyan 325 a duniya duk shekara.

2. Cutar kan zama cutar dajin dake kama huhu idan ba a gaggauta neman magani ba wanda hakan ke kawo ajalin mutane miliyan 1.34 a duniya.

3. Hepatitis B da C na cikin cututtukan da basa nuna alamu idan an kamau da su sai dai ta hanyar gwaji.

4. Wadannan cututtuka na da nasaba da kashi 60 bisa 100 na cutar dajin dake kama mutu da mutane ke fama da shi.

5. Matsalolin rashin yin gwaji da kula na cikin matsalolin da ya kamata a kawar da su kafin nan da shekarar 2030.

6. Yin gwaji da wuri da shan magunguna ne mafita daga wadannan cututtuka.

7. Cutar na iya kashe mutum farat daya idan ba a shan magani.

8. Ana iya kubuta daga kamuwa da cutar ko kuma a warke idan an kiyaye sharadun guje wa kamuwa da cutar.

9. Ana iya kamuwa da cutar idan ana amfani da kayayaki kamar su reza, abin aski da sauran sun a wanda ke dauke da cutar kokuma yawan kusantan wanda ke dauke da cutar na iya sa a kamu da cutar.

Abubuwa 7 game da maganin rigakafin cutar Hepatitis (Hepatitis B Vaccine)

1. An sarrafa maganin rigakafin cutar Hepatitis daga cutar Hepatitis wanda idan ya shiga jikin mutum yake kare shi daga kamuwa da cutar.

2. Wannan maganin na kare mutun daga kamuwa da Hepatitis B ne kawai.

3. Ana bada rigakafin maganin sau uku ko hudu na tsawan watanin shida domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

4. Za a iya yi wa jarirai allurar rigakafin wannan cutar wanda idan suka fara bayan an haife su za su iya kammala shi a lokacin da suka kai watanin shida da haihuwa.

5. Kamata ya yi yara daga shekaru 19 zuwa kasa su sami wannan rigakafin musamman wadanda tun farko basu taba yin rigakafin ba.

6. A yawaita yin rigakafi

7. Za a iya yin allurar rigakafin wannan cutar tare da sauran alluran rigakafi.

Share.

game da Author