PREMIUM TIMES ta gano wani shiri da hukumar NYSC ta ke kokarin yi don sabular da ministar harkokin kudi ta Kasa, Kemi Adeosun daga harkallar Satifiket din boge da buga cewa an dauke mata bautar kasa.
Wani jami’I a hukumar ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tabbas akwai shiri da ake kullawa don ganin ko ta halin kaka an samar da wata hanya da zai nuna cewa Kemi ba ta yi laifi ba.
“ Shirin da aka fara yi a farko shine wanda hukumar ta ce wai tabbas Kemi ta taba neman a dauke mata yi wa kasa hidima wanda tuni har hukumar ta sanar wa ‘yan Najeriya.
“ Suna so su nuna cewa ai bayan ta rubuta neman a dauke mata yi wa kasa hidima, wani ne a hukumar ya bata wannan Satifiket na boge, amma ba laifin ta bane. Daga nan sai ace za ayi bincike don gano wandanda suka aikata haka. Daga nan sai a nemi buga mata na gaskiya a bata.” Inji wani jami’in hukumar
Sai dai kuma a jiya Laraba ne tsohon shugaban hukumar NYSC din Janar Maharzu Tsiga, wanda ya fara aiki da NYSC a cikin Janairu, 2009, yayi tattaunawa da PREMIUM TIMES ta wayar tarho, daga gidan sa na Katsina.
Janar Tsiga mai ritaya, ya kara bayar da hasken da ya tabbatar da cewa satifiket din na Kemi na jabu ne.
Ya kara furta maganar da daya daga cikin tsoffin jami’an hukumar da suka yi aiki tare, da shi, Mista Ani ya fada cewa tantance sahihancin satifiket na NYSC ko kuma na bogi abu ne mai sauki.
Ya ce akwai daki mai na’urorin tantance komai, don haka bai ga dalilin da zai sa a bata lokacin wai sai an je wani ko wasu wuraren yin bincike ba, sai fa idan ba a son yin bincken kawai.
Maharazu Tsiga ne ya kamata a ce ya sa mata hannu, amma sai ya kasance satifiket din na dauke da sa hannun Bomai, wanda shi Tsiga din ya gada tun Janairu, 2019.
Satifiket din na Kemi Adeosun na dauke da sa hannun Bomai, kuma ya sa hannun a cikin watan Satumba, 2019, watanni tara cur bayan saukar da daga shugabancin NYSC.
Discussion about this post