Abin da ya sa ba mu watsa kasafin kudin mu kowa ya gani – Gwamnoni

0

Watanni da dama bayan sun bayyana kasafin kudaden sun a jihohi, kalilan ne daga cikin Gwamonin Jihohi ke watsa kasafin kudin da suka gabatar a kafafen yada labarai na yanar gizo domin jama’a su karanta.

Kungiyar sa-kai da ke nazarin kasafin kudi mai suna BudgIT ce ta fito da wannan binciken.

Daga cikin jihohi 15 da suka lika na su kasafin a yanar gizo domin karantawa, jihohi 13 ne kadai suka bayyana kasafin dalla-dalla.

Jihohin da suka bayyanar wa jama’a kasafin na su, sun hada da: Borno, Delta, Edo, Ekiti, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Kogi da Kwara.

Sai kuma Lagos, Nasarawa, Ondo, Plateau da Yobe.

Lagos da Kwara ne suka buga, amma ba su yi wani gamsashshen bayani dalla-dalla ba.

Jihohin da ba su buga komai domin jama’a su karanta a ‘online’ ba, sun hada da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Ebonyi, Enugu, Ogun da Osun.

Akwai kuma irin su Oyo, Sokoto, Taraba, Zamfara, Rivers, Niger, Kebbi, Jigawa da Imo.

Sai dai kuma kakakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya bayyana cewa sun rigaya sun buga jawabin kasafin kudin a cikin shafukan jaridu har ma da wasu shafukan soshoyal midiya.

Ya ce kuma idan aka bincika a shafin Ma’aikatar Kasafin Kudi, za a ga bayanin kasafin kamar yadda kuma idan aka buda shafin Majalisar Dokoki ta Jihar, nan ma za a ga cikakken bayanin.

Shi kuwa Terver Akase, Kakakin Gwmanan Jihar Taraba, ya ce bai ga wani amfanin buga kasafin a watsa a yanar gizo ba.

Ya kara da cewa kin bugawar ai ba ya na nufin gwamnati ta kasa ba ne.

Ya ce kasafin jihar a fili ya ke ba abu da ke boye ba. Don haka ko an buga ko ma ba a buga a ba, duk dai jama’a sun sani.

Shi ma kakakin Gwamnan Jigawa cewa ya yi bai ga amfanin buga kasafin kudin a shafin su yanar gizo ko intanet ba.

Share.

game da Author