A jam’iyyar APC babu ballallu ko baraka, mambobin R-APC ‘yan tuggu ne kawai – APC

0

Jam’iyyar APC ta fito karara ta maida wa hasalallun mambobin ta da suka balle suka kafa sabuwar jam’iyyar da suka rada wa suna R-APC.

Duk da wannan ballewa da suka yi, APC ta ce babu wata baraka a tsakanin mambobin jam’iyyar.

A ranar Laraba dai ne mambobin APC da suka fito daga PDP, suka balle suka kafa sabuwar jam’iyya a karkashin Buba Galadima da Zakari Baraje.

Galadima ya ce babu sauran wani burbishin adalci a cikin jam’iyyar APC, idan aka yi la’akari da yadda jam’iyyar ta gudanar da zabukan shugabannin ta na mazabu, kananan hukumomi da kuma na jihohi.

Sai dai kuma Sakataren Yada Labaran APC, Bolaji Abdullahi, ya jajirce cewa babu wata baraka ko wasu ballallu daga APC.

Ya ce kawai wasu gungun mutane ne suka tuma tsalle gefe daya su na neman kawo rudu a cikin jam’iyyar.

” Sannan zamu sa ido mu ci gaba da duba yadda abubuwa ke gudana domin kare mutunci da hadin kan jam’iyyar mu.

” Wadannan masu kirkiro sabuwar bangare a APC ba mutanen arziki bane sannan shiri ce kawai don su kawa baraka a jam’iyyar, amma mu a nan bamu san dasu ba, jam’iyyar mu na nan a daure tamau.

Ya kira su da sunan ‘yan tuggu masu neman kawo makarkashiya a cikin jam’iyya.

Share.

game da Author