Kotu ta bada belin Naira 200,000 ga barawon wayar Naira 80,000

0

A yau Alhamis ne kotun dake Badagry jihar Legas ta yanke wa wani mutum mai suna James Adavo hukuncin biyan belin Naira 200,000 a dalilin sace wayar wata mata mai suna Sevivi Balogun.

Lauyan da ya shigar da karar ya bayyana cewa Adavo ya sace wayar Sevivi ne ranar 11 ga watan Yuli dake Unguwar Ibereko dake Badagry a jihar Legas.

” Mutanen unguwa ne suka kamo Adavo bayan ya fizge wayar daga hannun Sevivi.”

Alkalin kotun Jimoh Adefioye ya bada belin Adavo kan Naira 200,000 sannan Adavo zai gabatar da takardun shaidun biyan haraji wa gwamnatin jihar Legas duk a ciki.

Share.

game da Author