2019: Dole fa sai APC ta ci zaben jihar Kwara – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa babu gudu, babu ja da baya a zaben 2019, tilas sai jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari sun yi nasara a jihar Kwara.

Lai Mohammed da dan asalin jihar Kwara ne.

A cikin wata takarda da ya fitar a jiya Litinin a Abuja, ya ce ganin yadda ake ta fita daga APC a jihar Kwara, akwai bukatar a karfafa jam’iyyar kuma a canja mata alkibla.

Sai ya kara da cewa kofa a bude ta ke ga duk masu sha’awar shiga cikin jam’iyyar, domin a kara mata karfi saboda zaben 2019.

Ya yi nuni da cewa fitar wasu fandararru daga APC a jihar Kwara, ya nuna ke nan jam’iyyar ta raba tsaki daga tsakuwa kenan.

Lai ya ce ba zai amince APC ta ci gaba da kasancewa a hannun masu fuska biyu ba.

Ya kara da cewa kalubalantar da Mista Bologun ya yi masa dangane da kawo wata gudummawa da shi Lai din ya samar a jihar Kwara, ba ta taso ba.

A jiya Litinin ne dai uwar jam’iyyar APC daga Abuja ta raba takardar sanarwar cewa an rushe shugabannin APC na jihar Kwara saboda alakar su da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Share.

game da Author