Kungiyar nan mai rajin neman a ceto ‘yan matan Chibok da Boko Haram suka sace, ta koka a kan yadda gwamnatin tarayya ke binne gawawwakin sojojin da Boko Haram suka kashe a cikin sirri, ba tare da ana sanar da jama’a an kashe sojojin ba.
Cikin wata takarda da shugabannin na ‘Bring Back Our Girls’ su uku suka saka wa hannu, Oby Ezekwesili, Aisha Yesufu da Florence Ozor, sun yi wannan bayani bayan da wasu hotuna suka bayyana, inda aka nuno ana binne wasu sojoji masu yawa a kaburbura da yawa.
An nuno hotunan ne kwanaki kadan bayan da sojojin suka karyata labarin kisan da Boko Haram suka yi wa sojoji 23.
Wannan kisan dai sojoji ba su bayyana shi ba, har sai bayan kwanaki uku da kafafen yada labarai suka yayata shi.
Sai dai kuma kakakin sojojin Texas Chukwu ya ce an kai harin, amma ba a kashe kowa ba, ‘yan jarida ne kawai suka kara wa harin gishiri.
Sai ga shi kuma daga baya an rika ganin wasu hotunan sojoji dauke da gawawwakin sojoji a bakin kaburbura kusan 23, kamar yadda aka ruwaito tun da farko cewa an kashe sojoji 23.
Kungiyar BBOG ta ce abin takaici ne da tashin hankali ganin yadda hukumar tsaro ta sojoji ke nuku-nukun boye kisan sojoji har ana binne su a asirce.
“Shin ba a ce mana sojoji sun gama da Boko Haram ba? To idan har sun gama da Boko Haram, me ke kawo mana hare-hare har ana kashe sojoji kuma?”
Daga nan sun nuna takaicin yadda Boko Haram ke ta kisan sojoji bayan an rigaya an bayyana cewa tuni an gama da Boko Haram.
Kungiyar ta nemi gwamnati ta sanar da duniya yawan sojojin da aka kashe a cikin watan Yuli, 2018. Yin haka zai sa iyalan su da ‘yan Najeriya samun saukin jimami da kokwanton musabbabin mutuwar sojojin. Sannan kuma kungiyar ta ce a buga sunayen su kuma a karrama su, duk kuwa da cewa babu ran su.
Discussion about this post