Dawowar Saraki, Gwamna Ahmed da Ibeto cikin PDP ya zo daidai lokacin bukatar su -Inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana farin cikin ta jin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed da Jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu, Musa Ibeto, sun koma PDP.

A cikin wasikar taya su murna da kuma yi musu lale marhabin da PDP ta fitar, ta nuna cewa dawowar ta su cikin PDP ya zo a daidai lokacin da ake bukatar kasancewar su a cikin jam’iyyar domin bada ta su gudummawar wajen kokarin dawo da martabar kasar nan.

Kakakin jam’iyyar PDP Kola, ya ce Saraki da Ahmed sun ci bakar wahala, kuma sun ci kwakwa a cikin jam’iyyar APC, wadda suka sha wahalar taimaka mata har ta samu nasara a zaben 2015.

PDP ta yi musu albishir da alwashin za a tafi tare da su, kuma za a ba su damar da ake ba kowane dan jam’iyya a cikin PDP.

Saraki da Ahmed duk ana zargin su da hannu a aikata fashi da makami da aka yi a garin Offa, zargin da dukkanin su suka ce karya ce da sharri gwamnatin APC ke kitsa musu.

Share.

game da Author