Sallamar ‘Yan shi’a da Kotu ta yi: Gwamnatin Jihar Kaduna zata daukaka kara

0

A yau Talata ne kotu a jihar Kaduna ta sallami wasu mabiya kungiyar IMN da aka fi sani da ‘Yan shi’a a Kaduna.

Alkalin Kotun Hon. Justice D.S Wyom ya bayyana cewa hujjojin da gwamnatin Kaduna ta bayar bai gamsar da kotu ba saboda haka ta sallami wadannan da ake tuhuma da wadannan laifuffuka da aka mika a gaban ta.

A dalilin haka, kotu da sallame su, kowa ya kara gaba.

Sai dai kuma wannan hukunci da kotu ta yanke bai yi wa gwamnatin Kaduna dadi ba, inda bayan an yanke wannan hukunci ta sanar cewa za ta daukaka kara nan take a babban kotun daukaka kara da ke jihar.

Kwamishinar Shari’a na jihar Umma Hikima ne ta sanar da haka a madadin gwamnatin jihar.

Ta ce alkalin da ya yanke wannan hukunci bai yi wa gwamnatin jihar adalci ba sannan bai bi hujjojin da suka mika gaban kotu ba yadda ya kamata.

Share.

game da Author