Jakadan Najeriya a kasar Afrika Ta Kudu Musa Ibeto ya ajiye aikin jakadancin sannan kuma ya koma PDP.
Musa Ibeto da tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja ne ya mika takardar ajjiye akin sa ne a ma’aikatar harkokin kasashen waje.
Bayan haka jam’iyyar PDP da kanta ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tabbas Ibeto ya dawo jam’iyyar.
Ibeto shine tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja a gwamnatin Babangida Aliyu kafin ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC a 2014.