Muna maraba da dawowar ka PDP – Atiku ga Saraki

0

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar yayi maraba da dawowar shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki jam’iyyar PDP.

Atiku ya bayyana haka a sakon taya murna da nuna farincikin sa ga Saraki da dawowa jam’iyyar PDP.

Atiku ya ce Saraki mutum ne da dole a jinjina wa ganin irin gudunmuwar da ya baiwa jam’iyyar APC.

Ya ce jam’iyyar PDP na yi masa maraba.

Idan ba a manta ba, a yammacin Talata ne shugaban majalisar dattawa ya bayyana wa duniya cewa daga yau fa ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP.

A wata doguwar takarda da ya saka wa hannu da kan sa Saraki ya ce duk da kokarin ganin hakan bai faru ba abin ya ci tura domin kuwa maimakon a sami daidaituwa a tsakanin sa da shugabannin jam’iyyar APC abun tabarbarewa ya dada yi.

” Na ga zama a APC ba zai haifar mini da da mai Ido ba, dole ya sa na yanke shawara ficewa daga jam’iyyar In koma inda aka san daraja ta kuma nake ganin zan iya ci gaba da siyasa ta a cikin kwanciyar hankali.”

Share.

game da Author