Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya fada komar jami’an EFCC a yau Talata.
An ce ya isa ofishin ne da ke Abuja, a tsakanin karfe 9 zuwa 10 na safe.
“A yanzu dai ya na dakin da ake binciken wadanda ake zargi.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES. Shi ma wani hadimin Ekweremadu ya shaida cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan ya na tare da jami’an EFCC, amma kuma bai ce ga lokacin da za a sallame shi ya koma gida ba.
Wata majiyar EFCC ta ce, “akwai wasu tambayoyin da mu ke so Ekweremadu ya amsa, wadanda suke da nasaba da harkallar kudade. Amma ba mu san lokacin da za mu sallame shi ba tukunna. Amma ko me kenan, nan da karfe 5 na yamma za mu san abin da ake ciki.
Ekweremadu shi ne mafi girman mukami a cikin jam’iyyar adawar kasar nan, PDP. Tun cikin makon da ya gabata ne aka gayyace shi da ya amsa tambayoyi a ofishin EFCC.
An yi tirka-tirka a makon da ya gabata ranar Talata, lokacin da jami’an EFCC suka yi wa gidan sa kawanya, suka hana shi fita.
Discussion about this post