Bincike ya nuna cewa yawan shan maganin dake kawar da kasala a jiki da na sa a kamu da cutar yawan mantuwa.
Cutar yawan mantuwa wato ‘Alzheimer’ cuta ce da zaka ga mutum haka kawai yana yawan mantuwa. Kusan komai sai ya manta, da zarar ka tambaye shi sai kaga ya ce maka au na manta.
An gano cewa yawaita shan maganin da ke kara karfin jiki da kau da gajiya na haddasa irin wannan cuta.
Alamomin cewa an kamuwa da irin wannan cuta na ‘Alzheimer’ cutar sun hada da rudewa, yawan mantuwa, ciwon jiki da sauran su.
Wasu likitoci a jami’ar ‘Exeter, King’s College’dake garin Landan, kasar Britaniya da na jami’ar Bergen dake kasar Norway sgudanar da wannan bincike.
Likitocin sun gargadi mutane cewa maimakon su rika shan irin wadannan magunguna da zai iya sa su kamu da irin wadannan cuta, su sha ‘Paracetamol’ kawai ya fi musu idan ya zama dole.