Mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara kan hana zaizayar kasa da kwararowar hamada Mansur Kaura ya bayyana cewa gwamnatin ta shuka itatuwa 24,000 a wasu kananan hukumomin jihar domin kawar da matsalar kwararowar hamada da ake fama dashi.
Kaura ya ce “Gwamnati ta shuka itatuwa 1,000 a kananan hukumomi 14 da wasu 10,000 a kananan hukumomi shida akan Naira miliyan 10.
” A zagaye na uku zamu shuka itatuwa a kananan hukumomin Bakura, Birnin-Magaji, Talata-Mafara, Shinkafi, Kaura-Namoda da Zurmi akan Naira Miliyan 10.
Sannan kuma ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki domin ta kare garuruwan jihar daga matsalolin zaizayar Kasa da matsalolin kwararowar Hamada.
” Muna kira ga mutanen jihar da su taimakawa gwamnati wajen shka itatuwa a muhallin su.” Kaura ya ce.