Rundunar ‘Yan sandan Babban Birni Tarayya, Abuja, sun bada samarwar damke gaggan ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane su 35.
Yace cikin su kuma akwai wadanda suka kware sosai wajen kwace wayoyin jama’a sosai. Akwai kuma masu wata irin mu’amala da za a iya fassarawa da kungiyoyin asiri.
Wadanda aka kama din sun hada da Henry Ikoro, Joseph Rapheal, Fridaya Moses, Godwin Onah, Isreal Akpan, Ezugwu Valentine, Osita Ajibo, Gambo Nana, John Yusuf, Kelvin James da wasu da dama.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bala Ciroma ne ya bayyana haka a yayin da ya ke wa manema labarai jiya Litinin a Abuja.
Ciroma ya ce Wasu daga cikin kayan da aka samu a hannun su, sun hada da motoci hudu, bindigogi hudu, bindigar wasan yara daya, sai makullan bude kowane irin kwado, adda, wuka, wayar hannu guda hudu da kuma kyamarar daukar hoto.
Ya ce da an kammala bicike za a za damka su ga shari’a domin a hukunta su.
A karshe ya roki jama’a a rika kai rahoton batagari a cikin al’umma ko wanda ba a yarda da mu’amalolin sa ba.
Ya ce sai an yi haka za a iya cin gagarimar nasara, domin ‘yan sand aba za su iya kawar da batagari ba, sai da taimakon jama’a.