APCn Kwara ta maida wa Oshiomhole, Mala da martani

0

Idan ba a manta ba a jiya Litinin ne jam’iyyar APC ta sanar da rusa shugabannin jam’iyyar na jihar Kwara.

Wadannan zababbun shugabanni dai duk ‘yan bangaren shugaban majalisar dattawa ne Bukola Saraki da gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da sakataren Jam’iyyar Mai Mala Bunu suka saka hannu a wannan takarda da ya sanar da rusa wadannan shugabanni na jam’iyya a jihar.

Jam’iyyar ta nada sabon shugaba na riko a jihar.

Sai dai kuma shugabanin jam’iyyar a Kwara sun bayyana cewa ba za su bi wannan umarni na uwar jam’iyyar ba.

A takarda da ta fitar, shugabannin sun ce basu san kowa ba a matsayin shugaban su idan ba Ishola Fulani ba.

Kakakin Jam’iyyar na jihar Kwara, Sulyman Buhari ya bayyana cewa ” Idan ba nuna fin karfi da nuna karfin Iko ba, ba a ce an sami matsala a da ba sai a yanzu.

” Muna nan akan bakan mu, kuma babu wanda zai nuna mana iko ya canza abin da akayi tuni har an manta. Fulani dai shine shugaban mu kuma shi muka sani.” Inji Buhari.

Rusassun shugabannin sunce idan abin ya gagara za su garzaya kotu.

Share.

game da Author