FARAUTAR SARAKI: APC ta kori shugabannin jam’iyyar na Jihar Kwara

0

A wata sabuwar salon farautar Saraki da jam’iyyar APC ta kitsa, a yammacin Litinin jam’iyyar ta sanar da koran zababbun shugabannin jam’iyyar na jihar Kwara.

Wadannan zababbun shugabanni dai duk ‘yan bangaren shugaban majalisar dattawa ne Bukola Saraki da gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da sakataren Jam’iyyar Mai Mala Bunu suka saka hannu a wannan takarda da ya sanar da koran wadannan shugabanni na jam’iyya a jihar.

Jam’iyyar ta nada sabon shugaba na riko a jihar.

Share.

game da Author