Buhari ya aika da zaratan dakarun Najeriya 1000 da jiragen yaki jihar Zamfara

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a aika zaratan dakarun Najeriya 1000 da jiragen sama na yaki jihar Zamfara domin gamawa da tsagerun ‘yan ta’adda da suka addabi mutanen jihar.

Wadannan dakaru sun hada da jami’an ‘yan sanda, Sojoji, Sibil difens, da sojojin sama.

A takarda da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya saka wa hannu ya ce tuni har babban hafsan sojojin saman Najeriya Abubakar Saddique ya isa garin Gusau inda ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar ranar Lahadi.

” Gwamnati ta dauki dan tsawon lokaci ne don a samu na’urar gano inda wadannan ‘yan ta’adda ke boya da kuma samar da manyan makamai domin tunkarar su.

Jihar Zamfara ta yi kaurin suna kan ayyukan ta’addanci, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran su.

An sace dubban shanu, an kashe mutane masu dinbin yawa sannan an kona kauyuka da dama a sanadiyyar ayyukan wadannan ‘yan ta’adda.

Jiragen saman yaki da zasu yi aiki a wannan yankuna zasu na tashi ne daga filin jirgin sama dake Katsina.

Buhari ya kuma yi kira da a daina maida harkokin tsaron kasa siyasa.

Sannan kuma takardar ta yi kira ga manema labarai da su dunga sara suna duban bakin gatari, su dai rubutun da zai rika nuna wadannan ‘yan ta’adda kamar wasu sarakuna ne. ” Tunda da ma can irin abin da suke so kenan domin su ci gaba da ayyukan su na ta’addanci.

Share.

game da Author