‘Yan sanda a jihar Enugu sun damke wani gogarman buga kudaden jabu, mai suna Collins Oputa.
An kama Oputa ranar 26 Ga Yuli, kamar yadda wani jawabi da kakakin jami’an tsaron Ebere Amaraizu ya fitar wa manema labarai.
Amaraizu ya ce ‘yan sanda ne su ka yi nasarar kama Oputa da suka ce dan kauyen Ohaji ne a jihar Imo, amma ya ke zaune a titin Fatimo Close, Ijegun cikin jihar Legas.
“An samu sa’ar kama shi bayan jami’an leken asiri sun yi masa kofar-raggo, bayan an samu labari da kuma tabbacin cewa ya na buga kudaden jabu, har ya na bayarwa ga dillalan sa su na shigar da su a cikin hada-hada.
Kakakin ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gabatar da shi a gaban shari’a, bayan an kammala gano sauran abokan harkallar sa.
Oputa ya amsa cewa ya na buga kudin jabu, amma kaddara da kuma shaidan ne suka kai shi ga aikata wannan laifi.
Ya yi alkawarin cewa zai tuba ya daina idan aka yafe masa.