Idan mutanen Kaduna bas u zabe mu ba, za mu tattara namu-ina-mu mu bar musu jihar – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun kafin ya zama gwamna yake rokon Allah ya bashi ikon yi wa talakawa aiki, “ Idan ba zan yi wa talakawa aiki ba, ina rokon Allah ya sa kada in zama gwamna, shi yasa na ke yi wa talakawa aiki”

El-Rufai ya fadi haka ne a hira da yayi da gidajen radiyoyin jihar Kaduna ranar Alhamis a fadar gwamnatin jihar.

El-Rufai yace su suna aiki ne wa talakawa ba attajiran jihar ba domin kuwa ba kaunar su suke yi ba.

“ Attajiran jihar Kaduna ba kaunar mu suke yi ba, saboda ba za mu basu kudi su kashe haka kawai ba, idan zasu fita zuwa kasashen waje ba ma basu dala 10,000 kudin guzuri. Mun ce mu baza mu yi haka. Kudaden jihar za mu yi wa talakawa ayyuka da su ne.

“ Ba za mu dunga jida wa ‘yan jarida kudi ba suna rubutun karya kan ayyukan da bamu yi ba muce mun yi.

“ Abubuwan da mukayi alkawari duk muna yin su, saboda haka ba za mu karaya da koarfe-korafen ‘yan adawa ba.

El-Rufai ya kara da cewa wadanda suka fice daga jam’iyyar APC dama can yan kashe mu raba ne, ba wai masu kishin jama’a ba.

Da suka ga cewa ba za su sami yadda suke so ba karkashin mulkin Buhari sai suka ar-arce gaba dayan su.

“ Mun sani sun bar wasu a jam’iyyar don su rika sanar dasu abin da jam’iyyar APC ke ciki sai dai abin da basu sani ba shine duk mun san su kuma muna ankare da su.

“ Ko da aka ce ai mun kori ma’aikata a jihar Kaduna, mun canza fasalin masarautun jihar mu da gyara kananan hukumomi, an yi ta cewa wai baza mu ci zabe ba. Gashi mun yi zaben Kananan hukumomi kuma ‘yar fara ta nuna. Sai da muka cinye kananan hukumomi 15 cikin 23.”

Yace gwamantin sa za ta ci gaba da yi wa talakawan Kaduna aiki batare da jin tsoron ko zata ci ko ba za ta ci zabe ba a 2019.

Share.

game da Author