Tsohon gwaman jihar Gombe, Abubakar Hashidu ya rasu yau Juma’a a garin Gombe.
Marigayi Hashidu ya rasu ne bayan fama da yayi da rashin lafiya.
Za ayi jana’izar sa a garin Gombe a yau Juma’a.
Hashidu yayi gwamna a jihar Gombe a 1999 zuwa 2003.
Bayan haka kuma ya taba rike ministan Albarkatun Ruwa a lokacin mulkin Ibrahim Babangida.
Marigayi Hashidu ya rasu yana da shekaru 74.