Dakarun Sojin Najeriya sun fatattaki maharan Boko Haram a Jagana

0

Babban Kwamandan Sojojin Burget ta 7 da ke Maiduguri, Birgediya Janar Bulama Biu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa sojoji da ‘yan sanda sun kori maharan Boko Haram da suka yi yunkurin mamaye garin Jakana.

Dandazon ‘yan Boko Haram ne suka yi kokarin kutsawa cikin garin dauke da muggan bindigogi.

“Kwarai, Boko Haram sun yi kokarin kutsawa su kai wa garin Jakana mummunan hari, amma mun murkushe wannan yunkuri na su. ” Haka Biu ya shaida wa NAN, tare da bada uzurin cewa zai kira ya kara yin bayani daga baya.

Wani dan sanda mai aiki a Jagana, wanda kuma ba ya so a bayyana sunan sa, ya ce Boko Haram sun kai farmaki a garin, amma sun kora su baya.

Shi ma wani mazaunin garin da ya arce yayin da Boko Haram suka kai farmakin, ya ce maharan su na da yawan gaske, domin cike da motoci 15 suka shiga garin.

Garin Jagana dai ya na da tazarar kilomita 50 ne kacal daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Garin ya na kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Share.

game da Author