Sanata Shehu Sani dake wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana wa manema labarai cewa yana nan daram dam a Jam’iyyar APC bai canza sheka ba.
Shehu Sani ya ce dama can shi ba wai yana korafi don ya fice daga APC bane, yana korafi ne don a gyara kurakuran da ake tafkawa.
” Toh gashi yanzu jam’iyyar ta sami shugaba nagari wanda yasan darajar kujerar sa sannan ya na kokarin ganin an gyaro barakar da aka samu tuntuni.
” Kuma hakan shine damuwar mu, tunda an dauko turbar gyara babu dalilin ficewa daga jam’iyyar APC.
” Dama can an danne mu ne an hana mu shan iska, amma yanzu mun sami sabon likita da yake kokarin seta kowa akan turbar da aka gina jam’iyyar APC.