FASHIN OFFA: ‘Yan sanda sun yi wa Saraki tambayoyi a ofishin sa

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun je ofishin sa, kamar yadda ya nemi su je can su yi masa tambayoyi, am aba wai shi ya kai kan sa ba.

Ya bayyana a shafin sa na tweeter cewa jami’an sun isa da misalin karfe 1:40 na rana, inda ya ce ya kara jaddada musu, cewa ba shi da wata alaka da fashin offa.

Dama kuma can baya Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugaban ‘yan sanda da ya nemi Saraki ya aika masa da bayanin sa a rubuce, kamar yadda ya yi tun wanncan lokacin.

Sabuwar kwatagwangwama ta kunno kai ne yayin da ‘yan sanda suka rubuta wa Saraki wasika a ranar 23 Ga Yuli, cewa ya kai kan sa washegari 24 Ga Yuli, domin ya kara yi musu cikakken bayani dangane da wasu wurare da suka ce ba su gane sosai a cikin wancan rubutaccen bayani da ya yi musu a baya ba.

To bayan an kai masa farmakin cafke shi a gida da safiyar Talata, 24 Ga Yuli, ya tsallake, har ya halarci zaman majalisa, sai Saraki ya rubuta wa Sufeto Janar wasika cewa, ba zai taba kai kan sa ofishin ‘yan sanda don a yi masa tambayoyi kan zargin fashin banki a Offa ba, sai dai Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris ya tura masa yaran sa su yi masa tambayoyi.

Haka Saraki ya maida wa shugaban ‘yan sandan a wata wasika da ya maida masa amsa, ranar Talata, 24 Ga Yuli.

PREMIUM TIMES ta bada labarin sammacen da aka tura wa Saraki inda aka ce ya kai kan sa a ranar Talatar da ta gabata, karfe 8 na safe.

Sai dain kuma tun kafin lokacin sai ‘yan sanda suka mamaye kofar gidan sa, da nufin yi masa kofar-raggo su kama shi.

Haka shi ma mataimakin sa, Ike Ekweremadu, jami’an tsaro sun yi wa gidan sa kawanya, aka hana shi fita.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa an ritsa su ne domin a hana su halartar zaman majalisa a ranar Talatar, gudun cewa a ranar dandazon mambobin majalisa za su yi wa APC fitar-farin-dango.

Jami’an yan sanda sun ce idan Saraki bai kai kan sa ba, to zai dandana kudar sa.

A yau PREMIUM TIMES ta samu kwafen martanin da Saraki ya maida wa hukumar ‘yan sanda, inda ya ce bazai kai kan sa ba, sai dai Idris ya tura masa yaran sa su tambaye shi a ofis din sa.

Bayanai sun tabbatar da cewa Saraki ya rubuta wasikar ne bayan tashi daga majalisa a ranar Talata, bayan sanatoci 15 sun fice daga APC, kuma wasu mambobi 36 sun kara ficewa daga jam’iyyar mai mulki.

Cikin wasikar, Saraki ya ce bai ga dalilin da zai kai kan sa ba, alhalin ya na da labarin cewa Shugaba Buhari ya umarci shugaban ‘yan sanda cewa Saraki ya bada bayani a rubuce, ko kuma idan akwai bukata ya tura masa yaran sa su yi masa tambayoyi.

Har ila yau kuma Saraki ya kara bayyana tsoron abin da ka iya samun lafiyar sa idan ya kai kan sa, ganin yadda aka turo masa garken ‘yan sanda suka kewaye gidan sa, da niyyar yi masa kamun-kazar-kuku.

Share.

game da Author