Abin kamar almara kwatsam da yammacin Alhamis, mataimakin gwamnan jihar Kaduna ya bayyana a gaban taron manema labari cewa zai hakura da kujerar mataimakin gwamna zai yi takarar sanata na yankin Kaduna ta Kudu a 2019.
ko da yake Bantex ya ce ba zai sauka daga kurar mataimakin gwamnan ba har sai bayan zabe. Zai ci gaba da zaman sa a matsayin mataimakin gwamna amma kuma yana farautar kujerar sanata din a jam’iyyar APC.
” A gaskiya ban ji dadin yin wannan shawara ba saboda tsananin kauna da mutuncin dake tsakanina da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai.
” El-Rufai ya nuna mini in hakura mu ci gaba da tafiya tare amma na gaya masa cewa yana bukatar irin mu a majalisa domin taimaka masa cin nasara a mulkin sa.