Wani ma’aikacin kiwon lafiya dake aiki a asibitin Zamako a jihar Filato mai suna Nyam Azi ya bayyana cewa asibitocin jihar sun cika makil da mutanen dake fama da sarar macizai.
Azi ya fadi haka ne ranar Alhamis da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Jos.
A bayanan da ya yi Azi ya ce a watanni takwas da suka wuce a asibitin da ya ke aiki kawai mutane 430 suka garzayo da sarar maciji, sannan cikin su 9 sun rigamu gidan gaskiya.
” A lissafe hakan na nuna cewa maciji kan sari mutane biyu kenan a duk rana.”
Azi yace lokaci na damina da muke ciki na daga cikin dalilan da yasa a ka sami yawan sarar macizai da kuma yadda yara ke cusa hannayen su a ramuka da sunan wai suna farautar beraye.
” A yanzu haka mutane na kwance a kan benci wasu a kasa saboda karancin wurin kwanciya, kuma duk saran macizai ne.
Azi ya ce sun sami gudunmuwar maganin sarar maciji daga dan majalisa JohnBull Shekarau da ya sa suka sami saukin wahalar da suke fama shi. Sannan yayi kira ga sauran ‘Yan siyasa da su taimakwa asibitocin jihar da maganin sarar macizai.